Wa’azin Maganar Allah zuwa ga duniya da kuma ta’azantarda mutanen Allah.


Maraba da zuwa Family Radio!

Muna cike da farinciki domin zuwanku Family Radio! Dukannin abin da kun gani, ko kuna karatu ko kuma kuna ji a wannan yanar gizo manufar shi ne domin ya koyar da ku ya kuma ta’azantadda ku. Ko kuna so ku karanta Littatafan mu ne ko kuma ku saurare shirye-shiryen da mun samar anan, dukannin wadannan suna samuwa ba tare da biya wani abu ba.
 
Muna murna da kyautar Allah ne ceto, wanda ya samar wa mutanensa kyauta kuma a yalwace. A Family Radio dai muna samar da kome da muke badawa tare da wannan kaida a zuciya mai cewa:…Kyauta kuka karba, kyauta ku bayar. Matta 10:8. Don haka, muna maku maraba. Ku kasance a sake domin anfani da dukan abubuwan da kun samu anan kuma bari Allah ya albarkace ku yayinda kuna karatu ko kuma kuna saurare maganarsa.
 
Addu’an mu shi ne Allah ya yi anfani da Maganarsa domin ya bude idanunku ga gaskiya. Allah ya sa Family Radio ta zama abin ta’aziya kuma karfafawa a gareku yayinda kuna tafiya kuna kuma bautan Allah cikin duniyan nan. Mun gode!

 
 
 


Family Radio Inc- ma’aikata ce da ba neman riba take ba- © 2014 Ana rike da dukan ikon mallaka.